Mu Zagaya Duniya

Mu Zagaya Duniya

Shirin Mu Zagaya Duniya na duba Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya a cikin mako. Ana gabatar da shirin ne a ranar Asabar da safe a kuma maimaita ranar Lahadi da daddare.

00:00
00:00

Resumen del episodio

Za a soma shirin daga yankin Asiya inda shugabannin ƙasashen China, da Amurka, da kuma Rasha suka fitar da sanarwar haɗin gwiwa da ke fayyace ƙudurorin da suka tattauna a kansu, bayan taron kwanaki biyu da suka gudanar a birnin Shenzhen, da ke kudu maso gabashin ƙasar Sin.

Episodios

570-

Mu zagaya Duniya, shirin da ke waiwaye kan wasu muhimman labaran da suka faru

Za a soma shirin daga yankin Asiya inda shugabannin ƙasashen China, da Amurka, da kuma Rasha suka fitar da sanarwar haɗin gwiwa da ke fayyace ƙudurorin da suka tattauna a kansu, bayan taron kwanaki biyu da suka gudanar a birnin Shenzhen, da ke kudu maso gabashin ƙasar Sin.

21 nov. 2026
569-

Bitar muhimman abubuwan da suka faru a wannan mako daga nan Rfi

A Najeriya,jam’iyyar APC mai mulki ta baiwa jami’an tsaro umarnin bincika da hukunta ƴan dabar da suka tarwatsa taron magoya bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi a jihar Legas jiya alhamis.

14 nov. 2026
568-

Wasu daga cikin muhimman labaran mako daga Rfi hausa

Shirin na wannan makon zai soma daga Amurka inda Jam’iyar Democrat ta kwace iko da majalisun dokokin Amurka, bayan da ta yi wa jam’iyyar Republican ta shugaba Donald Trump mummunan kaye a zaɓen tsakiyar wa'adi da aka gudanar ranar 3 ga wannan watan na Nuwamba.

07 nov. 2026
567-

Dalilan da yasa dangantaka tsakanin Nijar da Chadi ta yi tsami

Shirin Mu Zagaya duniya na wannan mako tare da Oumarou Sani, ya yi duba kan sake rincaɓewar alaka tsakanin Nijar da Chadi bayan da Yamai ta zargi N'Djamena ta zargi da kashe yan kasarta biyu a wani harin da ta kai da jirgi mara matuki yankin Agadas Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin....

31 oct. 2026
566-

Gwamnatin Najeriya ta ce ta shirya tsaf don tunkarar barazanar Ebola

Shirin Mu zagaya Duniya na wannan makon tare da Oumarou Sani ya yi duba kan matakan da Najeriya ke ɗauka don hana yaduwar cutar Ebola a ƙasar. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin......

24 oct. 2026